ESL: Uefa ta fara shirin hukunta Barca, Madrid da Juventus

Hukumar kula da harkokin wasannin ƙwallon ƙafar Turai UEFA, ta fara zaman ladabtarwa kan ƙungiyoyin Barcelona, Real Madrid da Juventus kan shigarsu a yinƙurin ƙirƙiro da gasar cin kofin Super League.

Ƙungiyoyin dai na cikin jerin ƙungiyoyi 12 da suka yi yinƙurin ɓullo da gasar, saidai tuni 9 daga cikinsu suka sanar da ficewa daga tsarin, yayinda aka bar Barcelona, Juventus da Real Madrid.

Uefa ta ce ta fara zaman yadda za a ladabtar da ƙungiyoyin uku, bisa zargin karya ƙa’idojin hukumar.

Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Talata, ta ce za ta sanar da karin bayani kan halin da ake ciki a nan gaba kaɗan.

Comments (0)
Add Comment