EU ta ci Temu tarar dala miliyan 232 kan gazawa wajen dakile haramtattun kayayyaki

Hukumomin Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) sun ci kamfanin kasuwancin intanet na Temu tarar dala miliyan 232 bisa zargin gazawa wajen hana sayar da haramtattun kayayyaki da kuma kayayyakin da ka iya jefa masu amfani cikin haɗari.

Matakin ya biyo bayan wani bincike da ya shafe kusan shekaru biyu, wanda hukumomin kare haƙƙin masu sayen kaya daga ƙasashen Turai 17 suka gudanar kan yadda kamfanin ke tafiyar da harkokinsa a nahiyar.

Masu binciken sun bayyana cewa Temu bai ɗauki isassun matakan da suka dace ba wajen hana wasu kayayyaki masu haɗari shiga kasuwarsa, ciki har da cajar wayoyi marasa inganci da kuma wasu kayan wasan yara da ake zargin na iya haddasa illa ga masu amfani.

Hukumomin EU sun ce kamfanin ya kasa tabbatar da cewa kayayyakin da ake sayarwa ta dandalinsa sun cika ƙa’idojin tsaro da kariyar mabukata da ƙungiyar ta gindaya.

A cewarsu, irin wannan sakaci na iya jefa lafiyar masu amfani cikin haɗari tare da karya dokokin kare haƙƙin mabukata da ke aiki a ƙasashen ƙungiyar.

Hukumomin sun bai wa Temu wa’adin zuwa watan Agusta domin ya gabatar da gamsasshen bayani tare da nuna matakan da ya ɗauka don magance matsalolin da aka gano.

Sun yi gargaɗin cewa idan kamfanin ya gaza gamsar da su, zai iya fuskantar ƙarin hukunci da matakan ladabtarwa daga hukumomin Tarayyar Turai.

Comments (0)
Add Comment