Fadar Gwamnatin Tarayya Ta Kwantar da hankalin ‘Yan Nijeriya Kan Faduwar Shugaba Tinubu A Turkiyya

Fadar Shugaban Ƙasa ta kwantar da hankulan jama’a kan lafiyar Shugaba Bola Tinubu, wanda ke ziyarar aiki a ƙasar Türkiye, bayan da ya yi tuntuɓe a wajen tarbar girmamawa a Ankara.

Bayanai sun nuna cewa abin ya faru ne sakamakon shudiyar tabarmar (blue carpet) da ba a shimfiɗa da kyau ba, kuma Shugaban ya ci gaba da dukkan shirye-shiryensa na hukuma ba tare da wata matsala ba.

An bayyana cewa Shugaban yana gudanar da tarurrukan diflomasiyya da shugabannin Türkiye, ciki har da ganawa da Shugaban kasar Recep Tayyip Erdoğan, sannan za a gudanar da taron manema labarai bayan kammala tattaunawar.

Ziyarar, wadda ita ce ta farko a hukumance ga Tinubu zuwa ƙasar, na da nufin ƙarfafa dangantakar Najeriya da Türkiye tare da faɗaɗa haɗin gwiwa a fannoni kamar kasuwanci, zuba jari, makamashi da tsaro.

Comments (0)
Add Comment