Fadar shugaban kasa ta fitar da jerin wadanda ba za su biya haraji ba, a fadin kasar nan.
A wata hira da aka yi da Shugaban kwamitin gyaran haraji, Mr Taiwo Oyedele a tashar Channels ranar Talata, 8 ga watan Satumba,2025.
Ya bayyana cewa sama da kashi 97 na yan Najeriya ba za su biya haraji ba kwata-kwata, Mr Taiwo ya bayyana jerin wadanda biyan sabon harajin ba zai shafe su ba kamar haka, masu karbar mafi karancin albashi na 70 zuwa kasa.
Wadanda kudin shigarsu bai zarce dubu 100 ba a wata, da ‘Yan kasuwa masu jarin kasa da Naira Milyan 2.
Kamfanoni da a da ake karbar haraji a hannunsu duk da kadararsu ba ta haura milyan 25 ba, yanzu sai kadararsu ta kai Naira Milyan 100 sannan za su biya haraji.
Wadanda ke biyan tarin haraje- haraje ma ba a bar su a baya ba, domin daga sabuwar shekarar 2026 za su fara biyan haraji daya tal, kuma mafi karanci.