Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana muhimmancin fafatawar wasan hamayya ta Clasico ga Real Madrid a fatan da take na lashe kofin Laliga a bana.
A ranar Lahadi ne Real Madrid ta doke Celta Vigo 3-2, inda yanzu maki hudu ne tsakaninta da Barcelona da ke jan ragamar teburin LaLiga.
Kocin ya ce wasan Clasico ne zai iya yanke hukunci kan hamayyar kofin LaLiga.
Idan Madrid ta samu sa’ar doke Barcelona zai kasance maki ɗaya ne tsakaninsu, yayin da ya rage wasa huɗu a kammala kakar bana.