Falana Ya Gargaɗi Gwamnatoci Kan Sulhu Da Ba Wa ’Yan Ta’adda Lada

Fitaccen lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana, ya gargaɗi gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da su daina yin sulhu ko ba wa ’yan ta’adda wata irin lada, yana mai cewa hakan ya saɓa wa dokar hana ta’addanci ta ƙasa.

Falana ya bayyana hakan ne a wani taron da Amnesty International ta shirya a Abuja, inda ya nuna damuwa kan yadda wasu gwamnatoci ke tattaunawa da ’yan ta’adda tare da yafewa waɗanda suka ce sun tuba.

A cewarsa, dokar hana ta’addanci ta Najeriya ta tanadi gurfanar da duk masu hannu a ayyukan ta’addanci a gaban kotu, maimakon yin sulhu da su ko ba su wata gata.

Ya ƙara da cewa, duk wanda ya taimaka wa ’yan ta’adda ko ya shiga harkokinsu ta kowace hanya na iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru masu yawa a gidan yari, kamar yadda doka ta tanada.

Falana ya yi kira ga hukumomin gwamnati da su tabbatar da cewa ana bin doka da oda wajen yaƙi da ta’addanci, tare da tabbatar da an hukunta masu aikata irin waɗannan laifuka ta hanyar da ta dace.

Comments (0)
Add Comment