Mutane da dama mazauna Babban Birnin Tarayya (FCT) sun bayyana damuwarsu kan ci gaba da hauhawar farashin tumatir, inda farashin babban kwando ya kai tsakanin Naira dubu 150 zuwa 170, lamarin da ya jefa masu sana’a da masu saye cikin mawuyacin hali.
Wani mai sayar da kayan lambu a kasuwar Suleja, Malam Isah Ado, ya bayyanawa shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa babban kwandon tumatir da ake sayarwa kan Naira dubu 85 zuwa 90 makonnin da suka gabata, yanzu ya haura zuwa Naira dubu 150 zuwa 170.
Ya danganta tashin farashin da ƙarancin amfanin kakar bana, asarar da ake samu bayan girbi, da kuma tsadar jigilar kayayyaki daga gonaki zuwa kasuwanni.
Sai dai mazauna Abuja da masu sana’ar sayar da kayan miya sun yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan da za su taimaka wajen bunƙasa noman tumatir da rage tsadar sufuri domin sauƙaƙa wa jama’a daidaita rayuwa.