Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya yi tashin gwauron zabo, bayan da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran ta gagara cimma matsaya, lamarin da ya ƙara tayar da hankula a yankin Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun nuna cewa farashin ɗanyen mai na Brent ya tashi da fiye da kashi bakwai cikin ɗari, inda ya kai dala 103 kan kowacce ganga, sakamakon fargabar rikici da kuma barazanar tangardar sufuri ta teku.
Tashin farashin na zuwa ne bayan da gwamnatin Amurka ta bayyana aniyar ɗaukar matakin rufe mashigar tekun Iran, wani muhimmin wuri da ake bi wajen jigilar mai zuwa sassa daban-daban na duniya.
Sai dai Iran ta mayar da martani cikin gaggawa, inda ta yi gargaɗin cewa za ta kai hari kan duk wani jirgin ruwan soji da ya kusanci mashigar Hormuz, tana mai jaddada cewa ba za ta lamunci haka ba.
Bayan kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump, na hana zirga-zirgar wasu jiragen ruwa, rundunar sojin Amurka ta yi karin haske, tana mai cewa matakin zai shafi jiragen ruwa ne da suka fito daga gaɓar tekun Iran ko kuma ke kan hanyarsu zuwa can.
Ta kuma bayyana cewa ba za a hana sauran jiragen ruwa daga wasu ƙasashe wucewa ta mashigar Hormuz ba, matakin da ake ganin na ƙoƙarin rage tashin hankali a yankin.
A nata ɓangaren, Birtaniya ta bayyana cewa ba za ta shiga cikin shirin Amurka na aiwatar da wannan mataki ba, lamarin da ke nuna bambancin ra’ayi tsakanin ƙawayen yamma kan yadda za a tafiyar da rikicin.
Duk da tarin dakarun Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya, Iran ta ci gaba da fitar da miliyoyin gangar mai zuwa kasuwannin duniya, duk kuwa da matakan takunkumi da ake ƙoƙarin kakabawa.
Rundunar sojin Iran ta sake jaddada cewa duk wani jirgin ruwa da ya yi yunƙurin kutsawa ta mashigar Hormuz zai fuskanci martani mai tsanani.
Sai dai Shugaba Trump ya bayyana cewa bai damu da barazanar Iran ba, yana mai cewa ko dai Iran ta dawo teburin tattaunawa ko kuma ta fuskanci sakamakon matakan da za a ɗauka.