Farashin man fetur ya tashi zuwa Nera 1,532 a kowace lita

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa matsakaicin farashin man fetur (PMS) ya tashi zuwa ₦1,532.93 a kowace lita a watan Afrilu 2026, daga Naira 1,288.54 da aka samu a watan Maris, wanda ya nuna ƙarin kashi 18.97% a wata guda.

Rahoton NBS ya kuma nuna cewa, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, farashin ya tashi daga ₦1,239.33 a Afrilu 2025 zuwa ₦1,532.93 a Afrilu 2026, wanda ya kai kashi 23.69% na ƙaruwa a shekara guda.

Binciken ya kuma bayyana cewa jihohin Yobe, Edo da Bauchi ne suka fi fuskantar tsadar man fetur, yayin da jihohin Niger, Sokoto da Katsina suka fi rahusa.

A wani ɓangare kuma, rahoton ya nuna cewa farashin man dizal (diesel) ya ƙaru da sama da kashi 50% a wata guda, inda ya tashi daga ₦1,648.06 zuwa ₦2,474.69 a kowace lita.

NBS ta ce wannan ƙaruwa na farashin man fetur da dizal na ci gaba da shafar farashi a sassa daban-daban na ƙasar.

Comments (0)
Add Comment