Shugaban Hukumar Gudanarwar Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN), Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ƙaddamar da sabon ginin tashar United Nations Humanitarian Air Service (UNHAS) da World Food Programme (WFP) a Filin Jirgin Sama na Janar Muhammadu Buhari da ke Maiduguri.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar, Ganduje ya bayyana tashar a matsayin muhimmin aiki da zai ƙarfafa ayyukan jiragen agaji tare da sauƙaƙa isar da tallafin jin ƙai ga al’ummomin da ke buƙata a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Ya ce sabon ginin zai taimaka wajen inganta ayyukan hukumomin agaji da kuma ƙara saurin kai tallafi ga waɗanda rikice-rikice suka shafa a yankin.