Ganduje Ya Barranta Kansa da Komawa NDC

Ganduje ya barranta kansa da komawa NDC

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya sake jaddada cewa yana nan daram a jam’iyyar mai mulki, yana mai cewa shi ba ɗan siyasar da ke yawo daga wannan jam’iyya zuwa wata ba ne domin biyan bukatun kansa.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana haka ne yayin da yake musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya koma jam’iyyar ta New Democratic Congress (NDC).

A wata sanarwa da tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Kano kuma tsohon shugaban ma’aikatansa, Muhammad Garba, ya fitar a madadinsa ranar Juma’a, Ganduje ya ce hotunan da ake yaɗawa na ƙage ne da aka shirya domin yaudarar jama’a, da tayar da rudani a tsakanin magoya bayan APC.

Sanarwar ta ce Ganduje ya kasance mai tsayawa kan akidarsa ta siyasa, kuma bai taɓa tunanin ficewa daga jam’iyyar APC ba, wadda ya taba jagoranta a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.

“Ba gaskiya ba ne, kuma babu wata hujja ta siyasa ko ta hankali da za ta nuna cewa Ganduje ya koma jam’iyyar NDC” a cewar sanarwar.

Comments (0)
Add Comment