Gidauniyar Aliko Dangote ta kaddamar da sabon Shirin Tallafin Karatu na shekara-shekara (Annual Education Support Initiative) mai darajar Naira biliyan 100, wanda zai kai ga zuba fiye da Naira tiriliyan daya a ilimi cikin shekaru 10. Shirin zai fara a shekarar 2026, tare da bada tallafi wa dalibai 45,000 a shekara, sannan ya karu zuwa 155,000, ya kuma kai tiriliyan 1.3 cikin shekaru goma.
Tallafin zai fi mayar da hankali kan daliban da suke karatun kimiyya, kirikira, fasaha da lissafi (STEM), inda dalibai 30,000 za su samu tallafin kudin makaranta, sannan 5,000 masu koyon sana’o’i za su samu kayan aiki. Hakanan an ƙaddamar da Dangote Girls Scholars don tallafawa ’yan mata 20,000 a kowace shekara tun daga aji daya na karamar sakandire (JSS1) zuwa jami’a.
Gidauniyar ta kuma fara horar da malamai 10,000 a bangaren kimiyya, kirikira, fasaha da lissafi (STEM), tare da aiwatar da shirin cikin adalci a duk kananan hukumomi 774 cikin haɗin gwiwa da hukumomin ilimi na fadin Najeriya.
Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa ya ware kaso 25 na dukiyarsa domin dorewar shirin, wanda ya yi daidai da manufar gwamnatin Shugaba Tinubu na ‘Renewed Hope’ ta gwamnatin tarayya.