Gomna Abba Ya Yaba Wa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnonin Jam’iyyar APC Kan Tallafin Naira Biliyan Takwas Ga Waɗanda Gobara Ta Shafa

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma gwamnonin jam’iyyar APC bisa amincewa da bayar da tallafin naira biliyan takwas domin tallafa wa ‘yan kasuwar da gobara ta shafa a Kasuwar Singer da ke Kano.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Tofa, ya fitar a ranar Litinin, gwamnan ya bayyana godiyarsa matuƙa, yana mai cewa wannan tallafi babbar gudunmawa ce ga ‘yan kasuwar da suka yi asarar dukiyoyinsu sakamakon gobarar.

Gwamnan ya ce tallafin ya ƙunshi naira biliyan biyar daga Gwamnatin Tarayya da kuma naira biliyan uku daga gwamnonin APC a faɗin ƙasar nan, yana mai bayyana matakin a matsayin wanda ya zo a lokacin da ya dace.

Ya ƙara da cewa kuɗaɗen za su taimaka matuƙa wajen rage radadin asarar da gobarar ta haifar ga ‘yan kasuwa da iyalansu, tare da farfaɗo da harkokin kasuwanci a kasuwar da lamarin ya shafa.

Haka kuma, ya ce matakin ya nuna jajircewar Shugaban Ƙasa wajen tallafa wa ‘yan Najeriya musamman a lokutan ƙunci da iftila’i, tare da yaba wa gwamnonin APC bisa nuna haɗin kai da ɗaukar alhakin da ya rataya a wuyansu.

Gwamnan ya tabbatar da cewa za a yi amfani da kuɗaɗen cikin gaskiya da riƙon amana, domin sake gina shagunan da gobarar ta lalata tare da bai wa waɗanda abin ya shafa tallafi kai tsaye.

An sanar da bayar da tallafin ne ta bakin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, yayin da ya kai ziyarar jaje zuwa Kasuwar Singer, inda ya isar da saƙon goyon bayan Gwamnatin Tarayya ga waɗanda gobarar ta rutsa da su.

 Gobarar, wadda ta auku a ƙarshen mako, ta lalata dukiyoyi na biliyoyin naira, inda shugabannin kasuwar suka kiyasta cewa fiye da yan kasuwa dubu ɗaya abu ya shafa, yayin da hukumomi suka ce fashewar batirin hasken rana ne ya haddasa lamarin, tare da jaddada buƙatar inganta kayan aikin kashe gobara domin kauce wa maimaituwar irin wannan iftila’i.

Comments (0)
Add Comment