Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Ba Wa Kowane Ma’aikacin Jihar Kano ₦20,000 Goron Sallah

Gwamna Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da bayar da tallafin goron Sallah na ₦20,000 ga kowane ma’aikacin Jihar Kano da ke mataki na 01 zuwa 14, ciki har da ma’aikatan ƙananan hukumomi.

An bayyana cewa tallafin na da nufin rage wa ma’aikata raɗaɗin matsin tattalin arziƙi tare da taimaka musu wajen gudanar da shirye-shiryen bukukuwan Babbar Sallah cikin sauƙi.

Tallafin zai shafi dubban ma’aikata a faɗin jihar, yayin da gwamnatin ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin inganta walwalar ma’aikata da tallafa musu a lokutan bukukuwa.

Comments (0)
Add Comment