Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya tabbatar wa da shugabannin PDP a jihar cewa ba shi da wani shiri na barin jam’iyyar ya koma APC mai mulki.
Gwamna Adeleke ya tabbatarwa dukkan masu ruwa da tsaki da shugabannin jam’iyyar cewa yana nan daram a PDP kuma zai nemi zango na biyu a zaɓen Osun na 2026.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed, ya fitar a ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa gwamnan ya faɗi haka ne wani taron masu ruwa da tsakin PDP da ya jagoranta a gidan gwamnatinsa ranar Laraba da daddare.