Gwamna Badaru ya aza harsashin gina tattalin arziki dana siyasar jihar Jigawa bisa turba mai kyau ga wanda zai gaje shi – Isa Gerawa

An gano cewa, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar a matsayinsa na dan siyasa kuma dan kasuwa ya aza harsashin gina tattalin arziki dana siyasar jihar Jigawa, bisa turba mai kyau ga wanda zai gaje shi.

Wani Jigo a jamiyyar APC Alhaji Isa Muhammad Gerawa ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai, jim kadan bayan ya karbar wasu jiga jigai da kuma magoya bayan jamiyyar NNPP da suka sauya sheka zuwa jamiyyar APC

Ya bayyana yawan shigowa jam’iyyar APC da akeyi da irin salon jagoranci na Gwamna Badaru Abubakar da kuma mutunta jamiyyar da kuma sauran magoya bayan jamiyyun adawa.

Alhaji Isa Gerawa ya kara da cewa a zaben 2019, jihar Jigawa ce kadai ba a gabatar da korafin zabe ba a gaban kotun.

Inda ya kara da cewar sauya shekar jiga jigan jamiyyar NNPP zuwa APC zai sake bata dammar lashe zaben 2023

Alhaji Isa Gerawa wanda kuma sanannan dan kwangila ne, ya bayyana gwamna Badaru Abubakar a matsayin gwamna abin misali a tsakanin takwarorinsa.

Wanda ya biya basukan yan kwangila tare da biyan kudaden yan kwangila da aka tabbatar da aiyukansu bisa tsarin yarjejeniyar aiyukan kwangila.

Comments (0)
Add Comment