Gwamna Badaru ya nada Abdulkadir Jinjiri a matsayin kwamishinan tarayya

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya mika takardar kama aiki ga tsohan shugaban ma’aikata na jiha Abdulkadir Jinjiri Dutse da aka nada a matsayin kwamishinan tarayya a hukumar karbar korafe korafen jama-a ta kasa.

Da yake mika takardar kama aikin, Gwamna Badaru Abubakar ya taya shi murnar samun wannan matsayi tare da fatan zai kasance jakadan jihar nan na gari.

Ya kuma bayyana nadin da cewar ya dace matuka bisa la’akari da kwarewa da kuma cancanta.

A jawabinsa, Jinjiri Dutse ya yabawa Gwamnan bisa bashi wannan dama tare da alkawarin yin aiki tukuru domin sauke nauyin dake kansa.

Comments (0)
Add Comment