Gwamna Lalong ya sassauta dokar kullen da aka sanya a yankunan jihar Filato

Gwamna Simon Lalong na jihar Plateau ya sassauta dokar kullen da aka sanya a yanunan kananan hukumomin Jos ta Arewa.

Gwamnan ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da darkaan yada labarai da hulda da jama’a na gwamnan, Makut Macham ya fitar a Jos.

Gwamna Lalong ya sanar da cewa, yanzu dokar kullen a jos ta arewa zata na aiki ne daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe, wadda zata farad aga yau Laraba.

Haka kuma yace an sanya dokar ne, a yayin zaman da kwamitin tsaro ya gudanar a gidan gwamnatin jihar dake Jos, biyo bayan kasha kashen da ake samu a jihar.

Haka kuma yace dokar kullen a Jos ta kudu da kuma karamar hukumar Bassa har yanzu tana nan daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Haka kuma gwamnan ya sassauta dokar da aka sanyawa masu amfani da baburan adedeta sahu.

Daga karshe, gwamnan ya godewa al’ummar jihar Plateau bisa bin dokokin da suke, haka kuma ya roke su da su cigaba da goyawa gwamnati baya, wajan ganin ta dawo da jihar yanda take.

Comments (0)
Add Comment