Gwamna Nwifuru Ya Dakatar da Kwamishinoni 25 da Hadimai 60 Saboda Rashin Halartar Muhimmin Taro

Gwamnan jihar Ebonyi, Mai Girma Francis Ogbonna Nwifuru, ya dauki matakin ladabtarwa kan wasu daga cikin mukarraban gwamnatinsa da suka gaza halartar wani muhimmin taron gwamnati, inda ya dakatar da jami’an gwamnati 85 daga bakin aiki.

Wadanda matakin ya shafa sun hada da Kwamishinoni 25, manyan mataimaka na musamman (SSA) 14, mataimaka na musamman (SA) 24, da manyan sakatarori (PS) 22.

A wata sanarwa da Mai magana da yawun gwamnan, Mr. Monday Uzor, ya fitar a daren Litinin, ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan rashin halartar wani muhimmin taron gwamnati, wanda gwamnan ya dauka da muhimmanci wajen tsara abubuwan more rayuwa ga al’ummar jihar.

“Gwamnan jihar Ebonyi, Mai Girma Francis Nwifuru, ya ba da umarni cewa jami’an da aka lissafa su tafi hutun aiki na wata ɗaya ba tare da albashi ba saboda gazawar halartar wani taron gwamnati mai matukar muhimmanci,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa an haramta wa wadanda aka dakatar su saka hannu a duk wata takardar gwamnati, tare da umarnin cewa su mika kadarori da duk wata takarda ta gwamnati da ke hannunsu zuwa ga manyan sakatarorin ma’aikatunsu nan take.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ke ƙoƙarin tabbatar da da’a da kyakykyawar shugabanci a cikin harkokin mulki. Gwamnan ya jaddada cewa ba za a lamunci sakaci, rainin hankali da rashin girmama ayyukan gwamnati daga wani jami’i ba, komai mukaminsa.

Wasu daga cikin Kwamishinonin da aka dakatar:

  1. Injiniya Stanley Lebechi Mbam
  2. Farfesa Leonard Uguru
  3. Dr. Mathew Nwobashi
  4. Hon. Victor Chukwu
  5. Barr. Ikeuwa Omebe
  6. Hon. Chidi Onyia
  7. Cif Sunday Inyima
  8. Hon. Stanley Ogbuewu (da sauransu)

Manyan Mataimaka da Sakatarorin da abin ya shafa sun hada da:

  1. Hon. Bassey Chukwu
  2. Mrs. Rose Ofoke
  3. Mr. Kerian Ofoke
  4. Dr. Sabinus Nwibo
  5. Dr. Lawrence Ezeogo
  • Mrs. Joy Mbam
  • Barr. Emmanuel Onwe (da sauran su)

Gwamna Nwifuru ya bayyana cewa matakin na nufin farfado da da’a da tsari a gwamnati, tare da karfafa jajircewa wajen yi wa al’ummar jihar Ebonyi hidima cikin gaskiya da rikon amana.

“Wannan gwamnati ba za ta lamunci sakaci da aiki ko kin bin doka da oda ba,” in ji gwamna ta bakin mai magana da yawunsa.

Sanarwar ta ce dakatarwar ta fara aiki nan take, kuma hakan zai ci gaba har na tsawon wata guda, tare da dakatar da duk wata alaka da takardun gwamnati ga jami’an da aka lissafa.

Comments (0)
Add Comment