Gwamna Uba Sani Ya Gargaɗi Makarantu Masu Zaman Kansu da Su Guji Yin ƙarin Kuɗin Makaranta

Gwamnatin jihar Kaduna ta gargaɗi makarantu masu zaman kansu a faɗin jihar da su guji yin ƙarin kuɗin makaranta ba tare da sahalewar gwamnati ba.

Cikin wata sanarwa da babbar darakta mai kula da makarantu masu zaman kansu na ma’aikatar ilimin jihar, Mercy Bainta Kude ta fitar ta ce gwamnati ba ta amince da yin ƙarin kuɗin makaranta ba tare da saninta ba.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da aka koma zangon farko na sabuwar shekarar karatu a ƙasar nan.

Sanarwar gwamnatin ta ce bai kamata makarantu masu zaman kansu su ƙara kuɗin makaranta ba a daidai lokacin da gwamnatin jihar ke shirin rage kuɗin makarantar.

Sanarwar ta ambato wasu ƙa’idoji bakwai da suka ce dole sai makaranta ta cika su idan tana son ƙara kuɗin makanta, ciki har da kai shekara uku bayan ƙari na ƙarshe da kuma amincewa ƙungiyar iyayen yara.

Comments (0)
Add Comment