Gwamnan Sokoto Ya Sanya Hannu Kan Kasafin Kudin 2026 Na Nera biliyan 758.7

Gwamnan Jihar Sokoto, Dr. Ahmed Aliyu, a ranar Juma’a ya sanya hannu kan Kasafin Kuɗin Shekara ta 2026 na Naira biliyan 758.7, ya na mai tabbatar da aniyar gwamnatinsa na hanzarta ci gaban dukkan sassan jihar.

An sanya wa kasafin suna “Kasafin Bunƙasa Rayuwar Al’umma da Tattalin Arziƙi”, wanda aka tsara domin ƙarfafa ci gaba mai ɗorewa, faɗaɗa ababen more rayuwa, da inganta rayuwar mazauna jihar.

Bayan sanya hannu kan kasafin, Gwamna Dr. Ahmed Aliyu ya yaba wa Majalissar Dokokin Jihar Sokoto bisa sauri da inganci da suka nuna wajen duba kasafin.

Ya ce, “Na tabbatar wa mutanen jihar cewa za a fara aiwatar da kasafin nan da nan domin tabbatar da gudanar da ayyuka da shirye-shiryen gwamnati cikin lokaci. Kasafin 2026 ya mai da hankali sosai kan sassan da ke tasiri kai tsaye ga jin daɗin jama’a.”

Daga cikin kasafin:

Kashi 41% an ware shi ga bangaren tattalin arziƙi.
Kashi 37% an ware shi ga bangaren zamantakewa.
Kashi 16%, wato Naira biliyan 122.73, an ware shi ga bangaren lafiya.

Muhimman ayyukan lafiya sun haɗa da:

Kammala Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Sokoto, Kasarawa;
Murtala Muhammad Specialist Hospital;
Inganta asibitoci a Binji, Tambuwal, da Sabon Birni.
Haka kuma, an tanadi motocin asibiti guda 21 domin ƙarfafa ayyukan gaggawa a fannin lafiya a jihar.

A bangaren ilimi, an ware N115.95 biliyan domin inganta yanayin koyarwa da koyo, gyara makarantu, da faɗaɗa ababen more rayuwa a manyan makarantu. A bangaren noma kuma, an ware N18.74 biliyan domin ƙara samar da abinci da inganta tsaro na abinci.

Gwamna Dr. Ahmed Aliyu ya bayyana kasafin a matsayin mai mayar da hankali kan ci gaban jihar, inda ya ce kashi 72% na kasafin an ware shi ne domin kashe kuɗaɗen gina jari, yayin da kashi 28% an tanadar domin kashe kuɗaɗen gudanarwa, bisa shawarwarin IMF da Bankin Duniya.

Ya ƙara da cewa, duk ayyukan da ke gudana ko aka kammala a ƙarƙashin gwamnatinsa an gudanar da su ba tare da bashi ba, wanda ya sa jihar ba ta da bashi.

Comments (0)
Add Comment