Gwamnatin Ghana ta dakatar da gidajen rediyo guda 9

Hukumar Kula da Kafofin Sadarwa ta Ghana, NCA, ta sanar da rufe gidajen rediyo guda tara a ƙasar, ciki har da wasu fitattun gidajen rediyon da ake tunanin suna da alaƙa da jam’iyyun hamayya, bisa zarginsu da karya dokokin watsa labarai na ƙasar.

A cewar NCA, masu gidajen rediyon sun gaza wajen ɗaukar matakin gyare-gyaren da aka su wa’adin kwana 30 su yi.

Hukumar ta ce gidajen rediyo shida daga cikin taran, “sun ƙi, ko kuma sun yi watsi da wa’adin da aka ba su ta hanyar ƙin ɗaukan matakin da suka dace kan abin da aka buƙata daga gare su.”

Sanarwa ta ƙara da cewa gidajen rediyon guda uku, waɗanda mallakar shugaban yankin Ashanti na jam’iyyr New Patriotic Party ne, an rufe su ne bisa karya wasu dokoki, ciki har da yaɗa shirye-shirye daga wuraren da doka ba ta amince ba.

Wannan matakin na zuwa ne bayan sanarwar NCA a watan Yuni cewa ta rufe gidajen rediyo 62 saboda laifuka daban-daban, wanda ya biyo bayan umarnin da ministan sadarwa na ƙasar, Sam George, inda ya umarci hukumar ta ɗauki mataki kan gidajen rediyon da suka karya doka.

A lokacin ne shugaban ƙasar, John Mahama ya shiga tsakani, inda ya buƙaci a ba gidajen rediyon wa’adin kwana 30 domin su gyara abubuwan da ake zarginsu.

Daga cikin abubuwan da ake zarginsu akwai ƙin sabunta lasisi, wuce ƙa’aidar yaɗa labarai da aiki ba tare da cikakken izini ba.

Comments (0)
Add Comment