Gwamnatin Jihar Gombe ta kori kamfanin Gombawa Motors Nigeria Limited daga tashar Ibrahim Dankwambo Mega Park, inda ta umarce shi da ya fice daga harabar tashar cikin awa 24.
A cikin takardar sanarwar mai kwanan wata 25 ga Yuni, 2026, wadda kamfanin Principal Facilities Management Limited ya sanya wa hannu, an bayyana cewa an ɗauki matakin ne bisa ƙudurin Kwamitin Kula da Mega Park saboda zargin maimaita karya ƙa’idojin gudanar da tashar, rashin bin dokokin aiki da kuma korafe-korafen da aka samu daga wasu masu gudanar da harkoki.
An kuma aika kwafin takardar ga GROCOL, Kwamitin Kula da Mega Park, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe, DSS da NSCDC domin ɗaukar matakan da suka dace.
Sai dai korar ta zo ne kwanaki biyu bayan Gombawa Motors ta bayyana goyon bayanta ga Farfesa Isa Ali Pantami, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce. Duk da haka, takardar korar ba ta danganta matakin da siyasa ba, sai dai ta jingina shi da zargin karya dokokin gudanar da tashar.