Gwamnatin Jigawa ta fara shirin dakile ambaliya bayan hasashen NiMet

Gwamnatin jihar Jigawa ta tura kwale-kwalen gaggawa guda 20 domin ƙarfafa ayyukan ceto da kwashe mutanen da ambaliyar ruwa ka iya shafa a yankunan da ke fuskantar barazanar ambaliya a jihar.

Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan muhalli, Alhaji Hamza Muhammad, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Dutse.

Hamza Muhammad, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban kwamitin fasaha na rage illar ambaliya a Hukumar Raya Kogin Hadejia Jama’are, ya ce matakin na daga cikin shirye-shiryen gwamnatin jihar na dakile illar ambaliyar ruwa kafin ta afku.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakin ne bayan hasashen da Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya, Nigerian Meteorological Agency (NiMet), da Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Ƙasa suka fitar kan yiwuwar ambaliya a shekarar 2026.

A cewarsa, gwamnatin Jigawa ba za ta yi wasa da bayanan hasashen ba, domin tana da burin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce tun daga watan Fabrairun wannan shekarar kwamitin fasaha ke aiki tukuru wajen rage illar ambaliyar ruwa ta hanyar ɗaukar matakan kariya da wayar da kai a yankunan da ke cikin haɗari.

Hamza Muhammad ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta fara aiwatar da manyan shirye-shiryen dakile zaizayar ƙasa da ambaliya ta hanyar dasa bishiyoyi, gyaran gurɓatattun filaye, tono magudanan ruwa da kuma share hanyoyin ruwa domin hana koguna yin ambaliya.

Ya ce gwamnatin na aiki tare da hukumomin da suka haɗa da National Emergency Management Agency (NEMA), UNICEF, Red Cross Nigeria da wasu jihohi maƙwabta domin samar da tsare-tsaren gaggawa na rage illar bala’in.

A nasa ɓangaren, Babban Sakataren Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA), Hannafi Yakubu, ya ce hukumar ta gudanar da shirye-shiryen wayar da kai domin sanar da al’umma hanyoyin kare kai daga ambaliya.

Ya bayyana cewa hasashen shekarar 2026 ya nuna cewa ƙananan hukumomi 11 a jihar za su iya fuskantar ambaliya, ciki har da Ringim, Taura, Jahun, Miga, Malam Madori, Kaugama, Kafin Hausa, Auyo, Hadejia, Guri da Kiri Kasamma.

A cewarsa, za a yi amfani da manyan kwale-kwalen gaggawar a yankunan ruwa masu zurfi, yayin da za a yi amfani da ƙananan kwale-kwale a wuraren da ruwan bai yi zurfi ba domin ayyukan ceto.

Ya kuma ce hukumar ta tanadi kayan abinci da sauran kayan tallafi domin taimaka wa mutanen da ambaliya ka iya raba da muhallansu.

Comments (0)
Add Comment