Gwamnatin Jigawa Ta Jaddada Kudurin Ta Na Inganta Harkokin Wasanni A Makarantu

Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Jihar Jigawa, Dr Lawan Yunusa Danzomo ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na inganta harkokin wasanni a makarantu.

Ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da yake karbar tawagar jaha na manyan makarantun sakandire da suka halarci gasar kwallon kwando ta duniya Milo shiyyar Arewa maso yamma.

Dr Lawan Yunusa Danzomo ya taya daliban murnar samun matsayi na biyu a gasar kwallon kwando da matsayi na uku a baje kolin al’adu.

Ya kuma yi kira gare su da su rubanya kokarinsu a gasa ta gaba sannan ya yabawa masu horarwa da malaman da suka jagoranci daliban domin samun nasara.

Tun da farko babban sakataren ma’aikatar, Malam Abba Mustapha Yola ya gabatar da daliban ga kwamishinan

Sakataren ya kuma gabatar da kofuna da sauran kyaututtuka. Kwamishinan ya bayar da gudunmuwar naira dubu dari ga mahalarta taron domin sanya Jigawa alfahari.

Comments (0)
Add Comment