Gwamnatin Jigawa za ta gina tituna masu tsawon kilomita biyar a Jami’ar Sule Lamido

Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da gina tituna masu tsawon kilomita biyar a Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa, a wani mataki na inganta ababen more rayuwa da walwalar ɗalibai da ma’aikatan jami’ar.

Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Muhammad Ibrahim, ne ya bayyana hakan a wani shiri na gidan rediyon Jigawa da aka gudanar domin waiwayar shekaru uku na mulkin Gwamna Umar Namadi.

Ya ce Gwamna Umar Namadi ne ya bayar da umarnin gina titunan domin sauƙaƙa zirga-zirga a harabar jami’ar tare da inganta yanayin aiki da karatu ga malamai da ɗalibai.

Farfesa Muhammad Ibrahim ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta bunƙasa gonar jami’ar domin tallafa wa bincike da koyarwa, tare da ware naira miliyan 150 domin taimaka wa jami’ar wajen samun amincewar Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ga wasu shirye-shiryenta na karatu.

Haka kuma ya ce gwamnan ya ba da umarnin gina babban ɗakin taro na jami’ar, wanda za a sanya wa suna Dan Modi Auditorium.

Mataimakin shugaban jami’ar ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta amince da gina Sashen Koyar da Shari’a da Dokoki (Faculty of Law and Sharia) a jami’ar domin faɗaɗa fannonin ilimin da ake koyarwa.

A cewarsa, gwamnatin Jigawa na ci gaba da ɗaukar nauyin horas da ma’aikatan jami’ar a fannoni daban-daban domin ƙara musu ƙwarewa, yayin da ta kuma samar da gidaje guda 26 ga malaman jami’ar.

Ya yabawa gwamnatin jihar bisa irin tallafin da take bai wa jami’ar, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen ɗaga darajar cibiyar da inganta harkokin ilimi a jihar.

Comments (0)
Add Comment