Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta ɗage dokar hana ɗaukar ma’aikata domin daƙile matsalar ficewar ƙwararru (brain drain) da ke shafar ƙananan hukumomi 27 na jihar.
Shugaban Hukumar Kula da Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Jihar Jigawa, DIG Uba Bala Ringim (mai ritaya), ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake yi wa ‘yan jarida bayani kan nasarorin da hukumar ta samu a shekarar 2025, a dakin taro na hukumar.
Ya ce hukumar ta samu gagarumar nasara a shekarar da ta gabata, ciki har da haɓaka mukamai ga ma’aikata 1,682, da kuma shirya bitoci da tarurrukan horaswa guda 163 da nufin ƙarfafa ƙwarewa, inganci da ƙarfin hukumomi a matakin ƙananan hukumomi.
Ya bayyana cewa daga cikin ƙalubalen da aka fuskanta akwai ƙarancin ma’aikata, inda ma’aikata 628 suka yi ritaya a shekarar da ta gabata a faɗin ƙananan hukumomi da hukumomin ilimi na ƙananan hukumomi.
A cewarsa, “Ma’aikata 72 na ƙananan hukumomi da ma’aikata 83 na hukumomin ilimi na ƙananan hukumomi sun rasu, haka kuma ma’aikata 704 na hukumomin ilimi na ƙananan hukumomi sun yi ritaya daga aiki.”
Ya ƙara da cewa yawan yin ritaya ba tare da saurin maye gurbi ba na raunana ƙarfin gudanarwa a ƙananan hukumomi.
Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu hukumar na da jimillar ma’aikata 6,322, kuma an samu raguwar kashi 20 cikin 100 na yawan ma’aikata sakamakon ritaya da mutuwa a shekarar 2025.
Malam Uba ya kuma ce Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da ɗaukar ƙarin ma’aikata a ƙananan hukumomi a shekarar 2026, domin ƙarfafa ingancin aiki da kuma inganta ayyukan hidima ga al’umma.