Gwamnatin jihar Zamfara ta sake bude makarantu 45 daga cikin 75 da ta rufe saboda rashin tsaro, kamar yadda ma’aikatar ilimi ta sanar yau Laraba a Gusau babban birnin jihar.
Babban Sakataren a ma’aikatar, Alhaji Kabiru Attahiru ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan kungiyar fasaha ta jihar kan harkokin ilimi a cikin gaggawa wadanda suka kai ziyarar neman shawara a ma’aikatar.
Kafin hakan dai Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe makarantun ne a watan Satumbar 2021 bayan sace daliban makarantar Sakandaren gwamnati da ke garin Kaya a karamar hukumar Maradun ta jihar.
Alhaji Kabiru Attahiru ya ce dukkan makarantun 75 sun fada cikin yanayin rashin tabbas a lokacin da aka rufe su.
Babban Sakataren ya yabawa kungiyar da ake kira da Education in Emergency a wannan ziyara tare da ba su tabbacin ma’aikatar ta kudiri aniyar ci gaba da hada hannu da duk masu ruwa da tsaki domin bunkasa harkar ilimi a jihar.