Gwamnatin Katsina Za Ta Tallafawa Ƴan Bindigar da Suka Tuba

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ta ɗauki matakin tallafawa ƴanbindigar da suka tuba ne domin ganin ta kawar da rashin ilimi da rashin aikinyi a tsakaninsu.

Hakan a cewarta na daga cikin dalilin da yasa suka shiga ayyukan da suka haifar da matsalar tsaro a jihar.

Kwamishinan tsaro na jihar, Dokta Nasiru Matazu, ya ce ƴanbindigan da suka tuban sun nemi gwamnati ta gina musu makarantu waɗanda ƴaƴansu za su dinga zuwa da asibitoci da kuma wuraren da shanunsu za su dinga shan ruwa.

Matakin a cewarsu zai taimaka wurin ganin cewa ƴanbindigar da suka tuba basu koma ruwa ba.

Sai dai masana a harkar tsaro na ganin akwai buƙatar tallafawa al’ummar da matsalar ta shafa irin wannan tallafin.

Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan sulhun da wasu al’ummomin jihar suka yi da ƴan bindiga a jihar.

Sai dai sulhun bai hana ƴan bindigar kai hare-hare, a sauran jihohin da ke makwabtaka da Katsinan ba.

Comments (0)
Add Comment