Gwamnatin ƙasar Malawi ta sanar da ɓullar ƙwayar cutar polio nau’i na biyu, bayan gano ta a wasu samfurorin muhalli.
Sakataren ma’aikatar lafiya da tsabta, Dan Namarika, ya bayyana cewa an gano ƙwayar cutar ne ta hanyar sa ido na yau da kullum kan ruwan magudanan bayan gida a wurare biyu da ke birnin kasuwanci na Blantyre.
Ma’aikatar lafiya ta yi gargaɗin cewa kwayar cutar na da matuƙar hatsari ga lafiyar jama’a, kuma tana iya haddasa shanyewar gabobi da ba ta warkewa, musamman ga yara, irin yadda kwayar cutar shan inna ta asali ke yi.
Ta ce duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da kamuwar cutar ga wani mutum ba, gano ƙwayar cutar a muhalli na nuna yiwuwar yaɗuwarta idan ba a ɗauki matakan kariya cikin gaggawa ba.
Gwamnatin ta bayyana cewa tuni ta fara ɗaukar matakan gaggawa, ciki har da ƙara sa ido, wayar da kan jama’a, da kuma shirye-shiryen ƙarin kamfen ɗin rigakafin cutar polio a wuraren da abin ya shafa.
Haka kuma, an buƙaci iyaye da masu kula da yara su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun karɓi dukkan allurar rigakafin shan inna domin kare su daga kamuwa da cutar.