Gwamnatin Tarayya ta amince da aikin jirgin ƙasa na cikin birnin Kano (Metropolitan Rail Service) mai tsabar kuɗi Naira tiriliyan 1, wani muhimmin aikin more rayuwa da ake sa ran zai sauya fasalin sufuri a birane tare da ƙarfafa bunƙasar tattalin arziƙin jihar.
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake jawabi ga mambobin tawagar Kano da suka halarci gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa ta shekarar 2025 da aka gudanar a Jihar Borno.
Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Laraba.
A cewar gwamnan, an tsara aikin jirgin ƙasan ne domin samar da ingantaccen, zamani kuma mai araha tsarin sufuri na jama’a, wanda zai haɗa muhimman yankuna a cikin birnin Kano, ya rage cunkoson ababen hawa, tare da sauƙaƙa zirga-zirga ga al’ummar jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce aikin na nuna sabuwar dai-dai tuwar siyasar gwamnatinsa da Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), inda ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin jawo muhimman ayyukan ci gaba zuwa Jihar Kano.
Ya bayyana aikin jirgin ƙasan birnin Kano a matsayin wani gagarumin tsoma baki da zai inganta rayuwar al’umma matuƙa, tare da mayar da Kano cibiyar sufuri da kasuwanci a Arewacin Najeriya.
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta yi aiki kafada da kafada da hukumomin Tarayya da suka dace domin tabbatar da aiwatar da aikin cikin sauƙi, gaskiya da riƙon amana, tare da tabbatar da amfanin aikin ga al’ummar Jihar Kano.
Haka kuma, ya nuna godiya ga Gwamnatin Tarayya bisa amincewa da aikin, yana mai jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen Tarayya ta hanyar manufofi masu kyau da bunƙasa ababen more rayuwa.