Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Sayen Tauraron Dan Adam Guda Biyu

Gwamnatin Tarayya ta amince da sayen sabbin tauraron dan adam guda biyu na sadarwa domin ƙarfafa ababen more rayuwa a fannin dijital a Nijeriya da kuma shirin Shugaba Bola Tinubu na bunƙasa tattalin arzikin ƙasa zuwa dala tiriliyan ɗaya.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Bosun Tijani, ya bayyana hakan a Abuja yayin taron Ranar Kare Sirri ta Duniya ta 2026, inda ya ce amincewar hakan zai kawo sauyi mai muhimmanci a dabarun dijital, duba da cewa Nijeriya ce kaɗai a Yammacin Afirka da ba ta da tauraron dan adam na sadarwa mai aiki.

Rahotanni sun ce sabbin tauraron za su taimaka wajen haɗa yankuna da dama, tare da cike gibin da ke hana faɗaɗa haɗin intanet, kuma tuni 60 cikin 100 na aikin ya kammala kuma an tanadi kuɗin kammalawa.

Ministan ya jaddada cewa faɗaɗa haɗin intanet dole ne ya tafi tare da ƙarfafa kare bayanai, yana mai bayyana Hukumar Kare Bayanai ta Ƙasa, NDPC, a matsayin ginshiƙi wajen gina amincewa da dorewar tattalin arzikin dijital.

A nasa jawabin, Kwamishinan hukumar NDPC, Vincent Olatunji, ya ce ɓangaren kare bayanai ya samu cigaba zuwa masana’antar naira biliyan 16.2, inda aka samar da dubban ayyukan yi da kuma ƙara kwarin gwiwar masu zuba jari sakamakon tsauraran matakan aiwatar da Dokar Kare Bayanai ta 2023.

Ya ƙara da cewa ƙarfafa tsarin kare bayanai ya bai wa Nijeriya karɓuwa a duniya, tare da lashe lambobin yabo da shiga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, yayin da Hukumar Sadarwa ta kasa ke shirin amfani da fasahar tauraron dan adam domin faɗaɗa wayar salula ga miliyoyin ‘yan ƙasa da har yanzu ba su samun isasshen ayyuka a yankunan da ke da wahalar kaiwa.

Comments (0)
Add Comment