Gwamnatin tarayya ta ce tana kokarin sanya Dalibai Miliyan 9 cikin shirin Ciyarwa a Makarantu

A wani Labarin kuma, Gwamnatin tarayya ta ce tana kokarin sanya Dalibai Miliyan 9 cikin shirin Ciyarwa a Makarantu karo na biyu.

A karkashin shirin, Daliban zasu rika samun Abinci a kullum, karkashin kulawar gwamnatin tarayya.

Ministar Ma’aikatar Jinkai, Iftila’i da Cigaban Al’umma Hajiya Sadiya Umar Farouk, ita ce ta bayyana hakan a lokacin da take tattaunawa da manema labarai a Abuja.

A cewarta, Daliban sun fito ne daga Makarantu dubu 54,619 a kasar nan baki daya.

Manema Labarai sun rawaito cewa Kimanin mutane miliyan ɗaya da cutar COVID19 ta shafa zasu samu tallafin Naira N5,000 duk wata na tsawon watanni shida.

Kazalika, Ministar ta ce Ma’aikatar jin ƙai da walwala na cigaba da aiki tuƙuru wajen aiwatar da shirye-shiryen tallafawa yan ƙasa domin cika ƙudirin shugaban ƙasa na tsamo yan Najeriya miliyan 100 daga cikin talauci a shekara 10.

Comments (0)
Add Comment