Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara biyan kuɗaɗen alawus-alawus na shekarar 2025 ga ɗaliban Najeriya da ke cin gajiyar shirin tallafin karatu na Bilateral Education Agreement (BEA) a ƙasashen waje.
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ta ce Babban Bankin Najeriya, Central Bank of Nigeria (CBN), ya riga ya tura kuɗaɗen da aka amince da su zuwa ofisoshin jakadancin Najeriya domin a fara rabawa ɗaliban da abin ya shafa.
Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, ya ce kuɗaɗen da aka fitar sun kai kaso 50 cikin 100 na bashin alawus-alawus na shekarar 2025, yana mai cewa ana ci gaba da shirye-shiryen biyan sauran kuɗaɗen.
A cewarsa, tuni aka sanya kuɗaɗen a asusun jakadancin Najeriya da ke ƙasashen da ɗaliban suke karatu, kuma ana sa ran fara biyan su nan take.
Ministan ya shawarci ɗaliban da su dinga bibiyar asusunsu domin ganin lokacin da kuɗaɗen za su fara shiga.
Alausa ya ce matakin ya nuna yadda gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ke bai wa jin daɗi da cigaban ilimin ɗaliban Najeriya muhimmanci a ƙarƙashin manufofin “Renewed Hope”.
Ya yaba wa ɗaliban da abin ya shafa kan haƙuri da juriyar da suka nuna yayin da suke jiran biyan kuɗaɗen, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa ɗaliban Najeriya da ke ƙarƙashin shirye-shiryen tallafin karatu.
Gwamnatin Tarayya ta kuma sake jaddada aniyarta ta ci gaba da cika dukkan haƙƙoƙin ɗalibai tare da bunƙasa manufofin da za su ƙarfafa ilimi, jin daɗin ɗalibai da kuma ci gaban ƙasa ta hanyar haɓaka jarin ɗan Adam.