Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamatin da zai yi duba kan gyare-gyaren da za’ayi wa shirin NYSC

An kaddamar da kwamatin wanda ya kunshi manyan masu rike da mukaman gwamnati, da mutane gama gari, da kuma yan kasuwa ne a ranar Talata a babban birnin tarayya Abuja.

Makasudin kafa kwamatin shine domin a lalubo hanyoyin da za’a inganta shirin na yiwa kasa hidima wato NYSC, da kuma duba kan yadda shirin zai zama yana da tasiri sosai ga cigaban kasa, sannan kuma ya zama ya yi daidai da muradan matasan kasar ta Najeriya.

Wannan matakin ya biyo bayan kiraye-kiraye da ake yi dangane da tsaro, mummunan muhalli, da kuma shi kansa shirin ya yi daidai da rayuwa da kuma tattalin arzikin kasar a abubuwan yau da gobe.

Da yake jawabi a yayin taron, Ministan cigaban matasa, Ayodele Olawande, ya ce shirin na NYSC ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa hadin kai a kasar, da kuma taimakawa matasa tun daga shekarar 1973 da aka samar da shi.

Comments (0)
Add Comment