Gwamnatin Tarayya tace bazata karɓi ƴanciranin Venezuela da Amurka za ta kora ba

Gwamnatin tarayya ta ce ba za ta amince ta karɓi mutanen da Amurka ke kora daga ƙasarta ba duk da irin matsin lambar da take yi wa ƙasashen Afirka, kamar yadda Ministan Harkokin Waje Yusuf Maitama Tuggar ya bayyana.

Da yake magana ta cikin shirin Politics Today a kafar talabijin ta Channesl TV, Tuggar ya ce Najeriya na da nata matsalolin da za su sa ba za ta karɓe su ba.

Ministan harkokin wajen kasar nan, Yusuf Tuggar ya ce Najeriya ba za ta lamunci matsin lambar da Amurka ke yi mata na karɓar ƴan ciranin Venezuela da Amurkan ke son ƙwasa tare da mayar da su Najeriya.

Matakin na Amurka na zuwa ne kwana biyu bayan da Amurka ta sanar da sauye-sauyen tsarin bai wa ƴan Najeriya bizar masu yawon buɗe ido da ƴan kasuwa, matakin da gwamnatin tarayya ta nuna rashin jin daɗinsa.

Gwamnatin Trump dai na ƙokarin kwashe baƙin hauren da suka je ƙasar, musamman baƙaƙen fata domin mayar da su wata ƙasa ta baƙaƙen fata. Tun bayan hawansa Mulki a karo na biyu, Trump ya yi alƙawarin korar baƙin haure miliyan ɗaya daga ƙasar.

Comments (0)
Add Comment