Gwamnatin Tarayya tace ta ba wa ‘yan kasuwa su dubu 25 tallafin kudi naira dubu 50-50

Gwamnatin Tarayya tace ta ba wa ‘yan kasuwa su dubu 25 tallafin kudi naira dubu 50-50 kowannensu, a wani bangare na shirinta na tallafin kudade ga kananan ‘yan kasuwa.

Darakta-Janar na hukumar kula da kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa ta kasa, Dikko Radda, ya sanar da haka a jiya a wajen kaddamar da shirin dabarun kasuwanci na kasa a birnin Sokoto.

Yace gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin horas da matasan ‘yan kasuwa su dubu 5 da 365 a fadin kasarnan.

Yace an zabo ‘yan kasuwa 145 daga dukkanin jihoshi 36 da babban birnin tarayya domin shirin, wanda zai mayar da hankali wajen habaka kananan da matsakaicin kasuwanci domin kawo sauyi a bangaren masana’antu, aikin gona da cinikayya.

Yace an tsara shirin a matsayin hanyar tallafawa kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa da basu horon dabarun kasuwanci da sana’o’i.

Comments (0)
Add Comment