Gwamnatin Tinubu za ta gyara gadar Legas kan Naira tiriliyan 3.6

Ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa gwamnati za ta gyara ginin gadar Third Mainland da ke Legas a kan Naira tiriliyan 3.6.

Ya ce barin gadar a mummunan yanayin da take ciki yanzu zai zama babban kuskure, domin gadar ce tafi kowacce samun zirga-zirga a kasar.

Ministan ayyukan ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Laraba bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a Abuja, inji rahoton Tribune.

Comments (0)
Add Comment