Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tattaunawa ta yi nisa da Saudiyya, Birtaniya, Amurka, Australia, da wasu ƙasashe domin samar da ayyukan yi ga ’yan Najeriya. Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi, Muhammad Maigari Dingyadi, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja ranar Talata.
A cewar ministan, wannan shiri na daga cikin tsare-tsaren gwamnati na magance matsalar rashin aikin yi da zaman kashe wando tsakanin matasa, in ji Leadership.