Hakeem Baba Ahmad Ya Shawarci Kwankwaso, Obi a kan su bawa Matasa dama su fito takara a Zaben 2027

Dr. Hakeem Baba Ahmad, tsohon mashawararcin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a kan harkokin siyasa ya nusar da Rabi’u Musa Kwankwaso da Peter Obi a kan zabe mai zuwa.

Hakeem Baba Ahmad ya ce kamata ya yi Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso su hakura da sake tsayawa takarar shugaban kasa Ya bayyana cewa sun yi kokari a baya, amma yanzu lokaci ya yi da za su ja daga gefe domin ba su da wani sabon abu da za su kara kawo wa Najeriya Baba-Ahmad ya nemi dukkan manyan ’yan siyasar da suka dade a fagen mulki, su ja gefe domin a ba matasa damar kawo canjin da kasa ke bukata.

Ya shawarci tsofaffin yan takarar shugaban kasa a jam’iyyun NNPP da LP da kada su tsaya takarar shugabancin Najeriya a 2027.A wata hira da ya yi da Trust TV, Baba-Ahmed ya ce lokaci ya yi da tsofaffin ‘yan takarar shugaban kasa za su ja daga gefe su bar matasa su fito takara domin a gyara kasa.

Comments (0)
Add Comment