Hanyoyin Zuwa Katsina Sun Zama Tarkon Mutuwa Saboda Hare-Haren ’Yan Bindiga

Matsalar tsaro ta sake tsananta a Jihar Katsina, inda hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane suka mayar da wasu manyan hanyoyin jihar tarkon mutuwa ga matafiya da direbobi.

Binciken jaridar Aminiya ya nuna cewa hanyoyi da dama da ke haɗa Katsina da sauran jihohi sun zama wuraren da ake yawan kai hare-hare, lamarin da ya sa matafiya da dama suka daina amfani da su saboda fargabar sace-sace da kashe-kashe.

Daga cikin hanyoyin da aka bayyana a matsayin mafi haɗari akwai hanyar Musawa–Matazu–Kafin Soli–Charanchi, Katsina–Dutsinma, Ƙanƙara–Faskari, Jibiya–Sakkwato da kuma hanyar ’Yantumaki–Dutsinma, wadda wasu direbobi ke yi wa laƙabi da “Ka bi ta da addu’a” saboda yawan hare-haren da ake fuskanta a cikinta.

Lamarin ya sake ɗaukar hankali bayan da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Ƙasa, Manjo Janar Rabe Abubakar Batsari (mai ritaya), tare da matarsa a hanyar Marabar Musawa zuwa Kafin Soli a Ƙaramar Hukumar Matazu.

Rahotanni sun ce shugaban wata ƙungiyar ’yan bindiga da aka fi sani da Kachalla Muhammadu Fulani ne ke jagorantar hare-haren da ake kai wa a yankunan Matazu, Musawa da wasu ƙauyuka makwabta, bayan da aka ce ya yi watsi da sulhun da aka yi da shi a baya.

Mazauna yankunan da direbobi sun bayyana cewa duk da ƙoƙarin jami’an tsaro, hare-haren sun sa mutane da dama sun koma amfani da hanyoyin da suka fi tsawo domin kauce wa fadawa hannun maharan.

Masana da al’umma sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara kaimi wajen tabbatar da tsaron hanyoyin domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

“Sanin kowa ne a halin yanzu gwamnati ta yi ƙoƙarin buɗe dukkan kasuwanninmu, kuma a yau babu hanyar da ba a bi a faɗin Jihar Katsina. Fatanmu shi ne, abubuwan da suka rage mu dage da addu’a da ƙoƙarin gano waɗanda ke yi mana zagon ƙasa ta fuskar tsaro domin sanar da gwamnati a lokacin da ya dace a ɗauki matakin da ya dace.”

Waɗannan su ne kalaman Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Malam Faruk Lawal Joɓe, a jawabinsa a lokacin da ya wakilci Gwamna Dikko Raɗɗa a ranar Hawan Sarki a shagalin bikin Babbar Sallah da aka yi a satin da ya gabata kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.

Comments (0)
Add Comment