Wasu da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe akalla mutane 17 a kauyen Guzamala-Abbari da ke Karamar Hukumar Guzamala, da kuma wasu sassan Karamar Hukumar Nganzai a Jihar Borno, lamarin da ya sake tayar da hankula a yankin.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Rt. Hon. Abdulkarim Lawan, wanda ke wakiltar mazabar yankin, ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya bayyana alhini tare da jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu.
Ya ce an gano gawarwaki 12 na mutanen Guzamala, inda aka yi musu jana’izar hadin gwiwa bisa koyarwar Musulunci a garin Monguno, yayin da aka binne wasu gawarwaki biyar da aka gano a wani kauye na Nganzai a garin Gajiram.
Shugaban majalisar ya bayyana kaduwarsa kan abin da ya kira kisan gilla da aka yi wa al’ummar yankin, yana mai cewa har yanzu ana ci gaba da bincike, kasancewar akwai mutane da dama da ba a gano makomarsu ba.
Ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda lamarin ya shafa, tare da yin addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata, da kuma rokon Allah Ya jikansu da rahama, Ya kuma dawo da zaman lafiya a yankin.
Gudumbali, hedkwatar Karamar Hukumar Guzamala, ta shafe shekaru da dama babu mazauna, kuma tana karkashin ikon ’yan Boko Haram, lamarin da ke hana dawo da cikakken ikon gwamnati a yankin.
Shugaban majalisar ya jaddada kiransa ga gwamnatin tarayya da rundunar soji da su kwato yankin Guzamala gaba daya, musamman ganin cewa kauyen da harin ya faru yana da tazarar kusan kilomita 15 ne daga Mairari, wani kauye da aka tsugunnar da jama’a a kwanakin baya.