Sarakunan Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero na shirin gudanar da hawan Daushe a yau Alhamis a birnin Kano, yayin da al’umma ke ci gaba da sanya ido kan yadda hawan biyu za su gudana saboda takaddamar sarautar Kano da ke gaban kotu.
Rahotanni sun nuna cewa kowanne daga cikin sarakunan zai fara hawan ne da misalin ƙarfe huɗu na yamma, inda ake sa ran Sanusi II zai zagaya wasu sassan cikin birnin Kano kafin ya koma fadar sa, yayin da Aminu Ado Bayero zai gudanar da nasa daga Mandawari zuwa Kwanar Dizo kafin komawa fadar Nasarawa.
Lamarin ya biyo bayan dawo da Sanusi II da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi bayan cire Aminu Ado Bayero, abin da ya haifar da shari’ar da har yanzu ake jira a kotun koli.