Hayaƙin janareto yayi sanadiyyar mutuwar mutum 7 a jihar Bayelsa

Mutum bakwai sun mutu sakamakon hayaƙin injin janareto da ya mamaye ɗakin da suke kwace a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa an samu gawarwakin mutanen galibinsu ɗaliban Jami’ar Niger Delta a cikin dakin kiɗe-kiɗe watau ‘studio’ ranar Talata da safe, bayan sun shaƙi hayaƙin injin.

Jaridar ta ce sutudiyan na ɗaya daga cikin mutanen da suka mutun ne.

An ce a ranar Litinin da daddare ne marigayan suka fara aiki a sutudiyan, sai barci ya ɗauek su sakamakon gajiyar da suka yi, ba tare da sun kashe injin ba.

Jaridar ta ce ko da gari ya waye ranar Talata, sai aka samu gawar mutum shida daga cikinsu, yayin da ɗayan ke cikin mawuyacin hali inda nan take aka garzaya da shi asibiti, kafin shi ma ya rasu a asibitin.

Hayaƙin janareta dai na ɗauke da wani sinadari da ke toshe hanyoyin shaƙar iska, lamarin da ke barazana ga rayukan mutane.

Comments (0)
Add Comment