Hedkwatar NSCDC ta lalata fiye da wuraren hakar ma’adanai 1,000 da ke aiki ba bisa ka’ida ba a Najeriya

Hedkwatar Hukumar NSCDC ta bayyana cewa ta lalata fiye da wuraren hakar ma’adanai 1,000 da ke aiki ba bisa ka’ida ba a fadin ƙasar nan cikin shekara guda.

Babban Kwamandan hukumar, Dr Ahmed Audi ne ya bayyana haka yayin wata ziyarar aiki da ya kai Jihar Jigawa domin duba ci gaban ayyukan rundunar.

Ya ce wannan kokari ya taimaka wajen ƙara kudaden shiga daga ma’adanai daga biliyan uku zuwa fiye da biliyan shida da digo tara a cikin shekara ɗaya.

Gwamna Umar Namadi ya yaba da ziyarar, tare da kiran ƙarin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin kare dukiyoyin kasa da inganta zaman lafiya.

Comments (0)
Add Comment