Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi gargaɗi ga ma’auratan da gwamnatin jihar ta shirya yi wa auren gata cewa ba za a amince da rabuwa ko saki tsakanin ma’auratan ba sai da sahalewar Hukumar Hisbah.
Daurawa ya bayyana cewa hukumar za ta sanya ido kan zamantakewar ma’auratan domin tabbatar da dorewar zaman aure da kuma rage yawaitar matsalolin da ke haddasa rabuwar aure.
Ya ce duk wani yunƙuri na neman saki ko rabuwa tsakanin ma’auratan da suka amfana da shirin dole ne ya bi matakan da Hukumar Hisbah ta tanada, yana mai jaddada cewa manufar shirin ita ce gina ingantattun iyalai masu ɗorewa a cikin al’umma.