Hukumar Hisbah ta Jihar Sokoto na ci gaba da gudanar da samame a wuraren da take zargin ana aikata alfasha da sauran ayyukan da ta ce sun saba da tarbiyya da koyarwar addini, a ƙarƙashin wani sabon shiri mai suna “Operation Tsaftace Birnin Shehu”.
A cewar hukumar, shirin na da nufin tsaftace birnin Sokoto daga abubuwan da take kallon a matsayin lalacewar tarbiyya da kuma kare matasa daga munanan ɗabi’u. A cikin kwanakin baya, jami’an Hisbah sun kai samame a sassa daban-daban na birnin, inda suka kama mutane da dama tare da rufe wasu wuraren da ake zargi da amfani da su wajen aikata baɗala.
An bayyana cewa samamen na gudana ne ƙarƙashin jagorancin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah na jihar, Malam Usman Abdullahi Jatau, tare da Daraktan Da’awah, Imam Sirajo Abubakar. Hukumar ta ce za ta ci gaba da ɗaukar irin waɗannan matakai domin tabbatar da abin da ta kira kiyaye ɗabi’u da martabar al’ummar jihar.
Shirin “Operation Tsaftace Birnin Shehu” ya kuma haɗa da hana wasu ayyuka da Hisbah ta ce na sabawa ƙa’idojin addini, ciki har da tsarin haya na “short time” a otel-otal da kuma wasu tarukan da maza da mata ke cakuduwa ba tare da bin ƙa’idojin Musulunci ba