Honarabul Abdussamad Dasuki ya nuna damuwa kan yadda ‘yan ta’adda ke ci-gaba da kisan al’umma a Sakkwato.

Dan majalisar Tarayya da ke wakiltar mazaɓar Kebbe/Tambuwal a majalisar wakilai, Honarabul Abdussamad Dasuki ya nuna damuwa kan yadda ‘yan ta’adda ke ci-gaba da kisan al’umma ba ƙaƙƙautawa a Sakkwato. 

Dasuki ya bayyana haka ne a jiya Litinin a yayin da yake jajantawa al’ummar mazaɓarsa a gundumar Kuchi da Jabo wadanda hare- haren ‘yan ta’adda ya shafa a kwanan nan.

Honarabul Dasuki wanda ya ziyarci wadanda lamarin ya shafa a sansanin ‘yan gudun hijira a Kuchi da ke Karamar Hukumar Kebbe da Jabo a Karamar Hukumar Tambuwal ya ba su tallafin agajin gaggawa na kayan abinci domin rage masu radadi.

Mataimakinsa kan harkokin majalisa Honarabul Attahiru Danmadi ne ya wakilci dan majalisar ya kuma tabbatarwa wadanda lamarin ya shafa kokarinsa kan daukar matakan da suka kamata domin tabbatar da tsaron rayukan su da dawowa da zaman lafiya a yankunan.

Ya ce yana kokarin ganin rundunar sojoji ta kara tura wadatattun jami’ai tare da tallafa masu domin yakar ‘yan ta’addan da wanzar da zaman lafiya a yankunan.

Comments (0)
Add Comment