Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta fara aikin yi wa mahajjatan bana allurar rigakafi a fadin jihar.
Wannan mataki na cikin shirye-shiryen aikin Hajjin 2025 domin tabbatar da lafiyar mahajjata kafin tafiya kasa mai tsarki.
Da yake kaddamar da shirin a cibiyar kula da lafiya ta farko da ke Hadejia, Darakta Janar na hukumar, Umar Labbo, ya bayyana kudirin hukumar na kare lafiyar mahajjata.
Ya bukaci mahajjata da su kasance masu bin doka da hakuri a duk tsawon lokacin aikin Hajji, tare da halartar dukkan tarukan wayar da kai da za su koya musu yadda za su gudanar da ibadar Hajj yadda ya kamata.
Labbo ya kara da cewa rigakafin ya hada da rigakafin sankarau, cutar shan inna da zazzabin cizon sauro, wanda dokokin lafiya na kasar Saudiyya suka wajabta.
Sawaba Radio na ruwaito cewa an fara rigakafin a duk kananan hukumomi 27 na jihar, inda Darakta Janar din ya sanya ido a wuraren rigakafin tare da bai wa wani mahajjaci allurar farko a cibiyar lafiya ta Hadejia.