Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa ta raba kayayyakin agaji ga manoman da ambaliya ta shafa a karamar Hukumar Kirikasamma

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa ta raba kayayyakin agaji ga manoman da ambaliya ta shafa a 2020 a karamar Hukumar Kirikasamma.

A jawabinsa wajen rabon kayayyakin a garin Turabu, babban jamiin hukumar Suleiman Saad Abubakar ya bukaci wadanda suka sami tallafin da su yi cikakken amfani dashi domin bunkasa noma.

Yace kayayyakin tallafin sun hadar da takin zamani da Ingantaccen irin Dawa da maganin kwari.

A jawabinsa mai baiwa gwamna shawara kan shigo da alumma cikin tsarin gwamnati Alhaji Hamza Muhammad Hadejia ya gargadi wadanda suka samu tallafin da su guji sayarwa inda kuma ya yabawa kokarin gwamnatin tarayya na rage radadi ga manoman da suka yi hasara a bara.

A jawabinsa shugaban Karamar Hukumar Kirikasamma Alhaji Isa Adamu Matara ya yabawa hukumar bada agajin gaggawa ta jiha bisa tallafawa manoman da suka gamu da iftilai a bara.

Comments (0)
Add Comment